Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran wato (AEOI) Muhammad Eslami ya bayyana cewa babu jada bayana a shirin nukliyar kasar iran, duk tare da takurawar kasashen yamma.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Eslami yana fadar haka a wani taro nay an jarida a nan Tehran a jiya Talata.
Ya kuma kara da cewa kasashen yamma masu babakere kan al-amura a duniya suna son haramtawa mutanen kasar Iran ilmin zamani da kuma ci gaba a fasahar Nukliya. Amma gwamnatin kasar Iran ta dage kan cewa yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar ba zai hana ta ci gaba da shirinta na makamashin nukliya ba.
A wani bangare a maganarsa, shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya bayyana cewa, hukumar IAEA da kuma kasashen yamma suna nuna fuska biyu a cikin ayyukansu, duk abinda ya shafi Iran suna tsanan tawa, amma ga HKI tana da makaman nukliya, kuma bata cikin yarjeniyar NPT ko kuma hukumar ta IAEA. Amma sai suyi kamar basu gani ba.
Don haka iran zata ci gaba da dagewa har zuwa lokacinda zasu tabbatar da hakkinta. Na mallakar fasahohin daban-daban.