Iran: A yau ne jagoran juyi ya jagoranci salla a kan gawar marigayi Ibrahim Raisi

Da safiyar yau ne jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci sallar janaza a kan gawar marigayi Ibrahim

Da safiyar yau ne jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci sallar janaza a kan gawar marigayi Ibrahim Raisi, tare da sauran abokan tafiyarsa da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgi, a ranar Lahadin da ta gabata.

An gudanar da sallar janazar ne a babban masallacin Juma’a na birnin Tehran da ke cikin jami’ar Tehran, tare da halartar manyan malamai da manyan jami’ai na dukaknin bangarorin gwamnatin Iran.

Baya ga haka kuma, taron sallar janazar ya samu halartar baki da jami’ai daga kasashen duniya daban-daban.

Bayan kammala taron da kuma rakiyar gawawwakin a birnin Tehran, za a mayar da su zuwa birannsu na haihuwa domin bizne su, inda za a bizne gawar marigayi shugaba Ibrahim Raisi a mahaifarsa birnin Mashshad.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments