A cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Iraki ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yace sun tattauna dangane da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto bayyana cewa a daren Asabar ne ministocin biyu suka tattaunawa kuma Aragchi ya fadawa Fuad Hussain na kasar Iraki, inda aka kwana dangane da tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa, ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Iraki sun tattauna kan yadda, kasashen biyu zasu kara dankonzamunce a tsakaninsu. Aragchi ya godewa kasar Iraki kan kokarinda take yi na tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Sannan Fuad Hussain ya bayyana cewa kasar Iraki tana goyon bayan tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.