Iraki: An Dakatar Da Tura Iskar Gas Zuwa Injunan Bada Wutan Lantarki A Yankin Kurdistan

Ma’aikatar Ma’adinai da wutan lantarki a yankin Kurdistan na kasar Iraki ta bada sanarwan cewa an dakatar da tura iskar gas zuwa cibiyoyin samar da

Ma’aikatar Ma’adinai da wutan lantarki a yankin Kurdistan na kasar Iraki ta bada sanarwan cewa an dakatar da tura iskar gas zuwa cibiyoyin samar da wutan lantarki a yankin saboda hare-haren da aka kai kan wata cibiyar hakar iskar gas a yankin.

Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa wani jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa ne ya fada kan cibiyar hakar iskar gas ta Kurmur, ta kuma jawo dakatar da tura iskar gas din.

Labarin ya kara da cewa jirgin ya fada kan cibiyar hakar iskar gas ta kurmur a bangaren Chemchel na lardin Sulaimaniyya ne, ya kuma haddasa barna mai yawa, wanda mai yuwa har da rasa rai ko rayuka.

A halin yanzu dai wadanda abin ya shafa suna kokarin ganin sun gyara barnan da harin yayi. Sannan tuna an fara bincike don gano daga inda jirgin yakin ya fito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments