Najeriya : Ana ci gaba da alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin. Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa. […]

Iran ta yi tir da Australiya kan alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci

Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,” “Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka […]

Ramaphosa ya soki Trump kan hana shi halartar taron G20 na badi

Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya soki kalaman takwaransa na Amurka Donald Trump na cewa ba zai gayyace shi taron kasashen gungun G20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya a shekara mai zuwa a Florida. Ramaphosa ya ce abin takaici ne yadda Trump ke ci gaba da daukar matakai bisa labaran da ba na […]

ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau

Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.” Wannan “juyin mulkin soja” ya zama […]

Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da cewa kasar a shirye take ta taimaka wa tarayyar Najeriya a fadan da take yi da ta’addanci. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha Maria Zakharova ce ta bayyana hakan, sannan kuma ta jinjinawa kokarin da gwamnatin ta Najeriya take yi a wannan fagen […]

Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da karbar gawawwakin shahidai 15 a jiya Laraba a karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni, da kungiyar agaji ta “Red Cross” ta shiga tsakani. Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Palasdinu ta kuma ce, daga lokacin da aka fara musayar zuwa yanzu,adadin gawawwakin shahidan da su ka karba sun kai 345, […]

Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki

Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.” Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon […]

Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa

Daya daga cikin ‘ya’yan babban malamin addinin musulunci a Najeriya Sayyid Ali Dhahiru Usman Bauchi ne ya tabbatar wa da jaridar “Daily Trust” rasuwar malamin. Sayyadi Ali ya furta cewa: ” Tabbas Shehi ya koma ga mahaliccinsa, mu duka daga Allah muke, kuma zuwa gare shi za mu koma.” Haka nan kuma ya kara da […]

HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin

Wata cibiyar bincike mai suna “Frensic Architecture’ ta bada sanarwan cewa, HKI tana fakewa da tsagaita budewa juna wuta a Gaza a matsayin dama ta sake shata kan iyakoki a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto cibiyar tana cewa a halin yanzu HKI ta maida ‘koren layin da Trump ya […]

Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa yawan Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke kashewa a Gaza yana karuwa duk tare da abinda suka kira tsagaiya budewa Juna wuta. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ma’aikatar na cewa a cikin sa’oii 24 da suka gabata sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 2 […]

An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki

Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan a halin yanzu yana birnin Bissau babban birnin kasar Gunea Bissau bayan da sojoji suka kwace mulki suka kuma hana shiga da fita daga kasar. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar da daruruwan masu sanya ido a zaben da aka gudanar a kasar a […]