Iraki: An bankado wani yunkurin kai wa masu ziyarar Arbaeen hari

Jami’an tsaron kasar Iraki sun sanar da gano wata kungiyar ‘yan ta’adda da ta yi niyyar kai wa masu ziyarar Arbaeen hare-hare, wanda aka shirya

Jami’an tsaron kasar Iraki sun sanar da gano wata kungiyar ‘yan ta’adda da ta yi niyyar kai wa masu ziyarar Arbaeen hare-hare, wanda aka shirya gudanarwa a kwanaki masu zuwa.

Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa, “tsarin da ‘yan ta’addan ke da shi sun hada da dasa ababen fashewa a kan hanyoyin da masu tattaki ke bi a yankin kudancin kasar da kuma saka guba a cikin kayan abinci da ake ba wa masu tattaki.

Har ila yau, bincike ya nuna cewa kungiyar ta’addanci ta ISIS ta yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen daukar wadannan mambobi nata da aka wanke wa kwakwalwa domin aiwatar da wadannan ayyuka.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, kungiyar na yin hakan ne ta hanyar yin amfani littafai da aka rubuta musamman domin tunzura masu irin wannan Akida ta kafirta musulmi da zubar da jinni, tare da yin amfani da wasu malamai masu irin waannan Akida domin gurbata tunanin matasa musulmi, da kuma saka su hanyar ta’addanci da sunan addini ko jihadi.

A ranar alhamis din da ta gabata ma  karamar hukumar Karbala ta sanar da kame wasu mutane 22 da suke Shirin kai hare-haren ta’addancin da suka tsara a lokacin tarukan  ziyarar Arbaeen na wannan shekara.

Ko a shekarun baya an yi ta samun irin wadannan matsaloli na ta’addanci daga kungiyoyi masu dauke da akidar takfir da suke kafirta al’ummar musulmi tare da halasta jininsu, inda suke Kallon dukkanin musulmi da ba su a  cikinsu a matsayin ‘yan bidi’a mushrikai ko kafirai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted