Hukumar Bada Lamuni Ta Duniya Ta ce Ƙarin ƴan Najeriya Miliyan 60 Sun Fada Cikin Talauci

Rahotanni sun bayyana cewa  Hukumar bada lamuni ta duniya, IMF ta ce canje-canjen da gwamnatin Najeriya ke yi na karfafa tattalin arzikin kasar, yasa  karin

Rahotanni sun bayyana cewa  Hukumar bada lamuni ta duniya, IMF ta ce canje-canjen da gwamnatin Najeriya ke yi na karfafa tattalin arzikin kasar, yasa  karin ƴan Najeriya sama da miliyan 60 sun fada cikin talauci a kasar.

Wata sanarwar da IMF ta fitar ta ce, wadannan sauye sauyen da shugaban kasar Bola Tinubu ya aiwatar a cikin shekaru uku, da suka hada da cire tallafin mai da sakin mara ga hada hadar kudaden waje da kuma daidaita tsarin karbar harajin kasar sun taimaka sosai.

IMF ta ce talauci ya dade ya na yawo a tsakanin ƴan Najeriya, yayin da rahotan Bankin Duniya ya ce yanzu haka kashi 69 na mutanen kasar na fama da talauci, wanda adadin kari ne a kan kashi 40 da ake da shi a shekarar 2019.

Hukumar ta yi gargadin cewar hauhawar farashin abinci da takin zamani da kuma tashin farashin man fetur na iya samarwa kasar karin kudaden shiga, tare da jefa talakawa cikin kunci, abinda ta ce zai jefa karin jama’ar Najeriya cikin talauci da kuma karancin abincin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted