A rana ta 21 da Isra’ila ta sake komawa yaki da al’ummar Falasdinu a Gaza, jiragen yakinta sun kai hare-hare munanan a yankin Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da kuma jikkata wani adadin Falasidinawa mai yawa.
Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai kungiyar Hamas ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami akan matsugunin ‘yan share wuri zauna a Asqalan da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar ‘yan sahayoniya.
A gafe daya ana gudanar da yajin aiki na gama gari a yankin yammacin kogin Jordan saboda nuna kin amincewa da yadda ‘yan sahayoniya suke yi wa al’ummar Falasdinu kisan kiyashi. Kungiyoyin fararen hula ne su kirayi wannan yajin aikin, wanda ya game yankin na yammacin kogin Jordan.
A wani labarin daga Gaza, ma’aikatar kiwon lafiya ta sanar da cewa da akwai mutanen da sun haura miliyan biyu da suke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Ma’aikatar ta yi wannan sanarwar ne adaidai lokacin da ake raya ranar lafiya ta duniya, tana mai kara da cewa; a kowane lokaci yanayin kiwon lafiya a zirin Gaza yana kara tabarbarewa.” Haka nan kuma ta yi gargadi akan rufe dukkanin hanyoyin shigar da abinci cikin yankin da hakan yake jefa rayuwar yara masu yawan gaske cikin hatsari.
Wani batu da hukumar kiwon lafiya ta yankin na Gaza, ta yi gargadi a kansa, shi ne yadda Isra’ila ta hana a shigar da riga-kafin shan inna cikin yakin, da hakan zai rusa kokarin da aka yin a watanni 7 a baya na fada da wannan cuta.