Rundunar IRGC Tana Shirya Kalubalantar Makiya Iran

Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Sararin samaniyar Iran jan layi ne ga rundunar sojin ƙasa Babban Kwamandan Rundunar Tsaron

Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Sararin samaniyar Iran jan layi ne ga rundunar sojin ƙasa

Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Ahmad Wahidi ya jaddada cewa: Sararin samaniyar Iran jan layi ne ga sojojin kasar, yana mai gargadin cewa: Duk wani keta sararin samaniyar kasar zai fuskanci mayar da martani mai karfi da kuma hukunci mai tsauri.

A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin “X”, Manjo Janar Wahidi ya rubuta cewa: Rundunar IRGC ta yi gargadin cewa: Sararin samaniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran jan layi ne ga sojojin kasar, yana mai jaddada cewa: Duk wani keta sararin samaniyar Iran da wata kasa ko mai kai hari zai yi, ba zai rasa amsar da ta dace ba, kuma martanin da zai gamu da shi mai karfi ne da zata zama mai tsananin radadi daga mujahidan Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted