Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Litinin ce, Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, suka rufe shagudansu da harkokin kasuwancinsu da kuma ofisoshinsu don neman HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da suke yiwa yan uwansu kuma yan kasarsu a Gaza. Amma kamar yadda jami’an tsaron HKI ta hanasu zanga zanga a wasu wurare, jami’an tsaron gwamnatin Falasdinawa a yankin ma, karkashun shugabancin Mahmood Abbas sun yi dirar mikiya a kan masu zanga-zanga harma sun kama wasu daga cikinsu sun tsare.
Majiyar kungiyar Hamas ta kara da cewa wannan dabawa kungiyar wuka a baya ne. Ta ce gwamnatin Falasdinawa a Ramallah tana wa yahudawan HKI aiki, tana taimaka mata wajen kissan falasdinawa a Gaza.