Hamas: Babu Wani Karin Tattaunawa Da HKI, A Aiwatar Da Yarjeniyar Kamar Yadda Take

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar

Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar tsagaita wuta da aka cimma da HKI dangane da yaki a Gaza ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmoud al-Mardawi wani babban jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘ba zamu tsawaita kashi na farko na yarjeniyar ba, haka ma ba za mu amince da gabatar da sauye –sauye a cikin yarjeniyar ba. Mardawi yace HKI za ta karbi fursinonin da suka rage a hannun Hamas kadai ne, ta hanyar ko tsarin da yarjeniyar ta amince da shi. Ya ce: Benyamin Natanyahu yana, cikin dimwa idan ya na son amfani da yunwa a matsayin makami don samun abinda ya kasa samu da makamai ba. HKI ta bada sanarwan cewa za ta dakatar da dabbaka yarjeniyar sulhu da Hamas bayan an kammala kashi na farko na Yarjeniyar, kuma zai dakatar da shigar abinci yankin Gaza idan an kammala kashi na farko na yarjeniya.

Kafin haka Netanyahu ya ce ya amince da shawarar da jakadan shugaban kasar Amurka Donal Trump, Steve Witkoff ya gabatar na tsawaita bangare na farko a yarjeniyar saboda watan Ramadan.

Kakakin kungiyar Hamas Hazem Wassem ya ce: kungiyar tana tuntubar masu shiga tsakani a aiwatar da yarjeniyar , a kai a kai, don ganin al-amura sun koma kamar yadda yakamata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments