Ministan Ruwa na Habasha Habtamu Etfa ya jaddada cewa, babbar madatsar ruwa ta kasarsa amfanin dukkanin kasashen yankin ne.
Etfa ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kamar yadda shafin yanar gizo na Ethiopian Monitor ya bayyana cewa, ” kwararar kogin Blue Nile ya karu a lokacin noman rani, yayin da muka ga raguwar ambaliya da kuma jinkiri fiye da wata guda.” Ya jaddada cewa abin da muke hasashe kuma muke bayyanawa yau da kullun ya tabata a aikace.”
Ya kara da cewa, “Grantin Renaissance Dam na Habasha ba kawai ya kara yawan filayen noma da ake nomawa a kasashen da ke gabar kogin Blue Nile ba, har ma ya taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyi daga bala’in ambaliya da ke barazana ga yankin.”
Bayanin na Ministan Ruwa na Habasha ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar tashe-tashen hankula a yankin game da sarrafa ruwan Nilu, inda Habasha ke fuskantar suka daga kasashen Masar da Sudan dangane da tasirin da madatsar ruwan ke da shi kan raguwar Ruwan da ke kwarara a cikin kasashensu.