Gwamnatin Yamen Ta Gargadi HKI Da Amurka Kan Cewa Tana Sa Ido A Kan Abinda Ke Faruwa Da Tsagaita Wuta A Gaza

Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta gargadi HKI da kuma Amurka kan cewa, tana sanya ido a kan yadda suke sabawa yarjeniyar budewa juna wuta

Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta gargadi HKI da kuma Amurka kan cewa, tana sanya ido a kan yadda suke sabawa yarjeniyar budewa juna wuta da suka cimma da su. Musamman yadda HKI ta sabawa yarjeniyar a mashigar Rafah na barin abinci ya shiga Gaza, da kuma bukatar sake tattauna wasu al-amura a yarjeniyar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran nakalto Hazem Al-asad mamba a majalisar siyasa ta kasar Yemen, yana fadar haka, ya kuma kara da  cewa, kungiyar a shirye take ta sake shiga yaki da Amurka, a duk lokacinda suka yi kokarin cutar da mutanen Gaza.

Al-Asad ya gargadi gwamnatin Amurka da masu goyon bayan HKI a duk wata cutarwa da zata yiwa mutanen Gaza.

Har’ila yau, wani mamba a majalisar, Nasir-Addeen Amir ya bayyana cewa idanummu na kan abubuwan da suke faruwa a Gaza, sannan hannayenmu suna kan na’urorin bude wuta a kan dukkan abubuwan da suka shafi HKI da Amurka, don kare mutanen Gaza.

Amir ya kara da cewa dukkan makamai masu linzami na kasar Yemen su na cikin shirin komawa yaki idan HKI ko kawayenta suka sake farwa mutanen gaza.

Ya kuma kammala da cewa mayakan ansarullah za su sake budewa jiragen ruwa masu zuwa HKI wuta a tekun maliya da sauran wuraren da ta kaiwa hare-hare a baya bayan an fara yakin Octoban shekara ta 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments