Gwamnatin kasar Iraki ta yi Allah wadai da matakin da Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta dauka na mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da kuma gine-gine matsugunan yahudawa ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba
Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Iraki ta bayyana Allah wadai da amincewa da kudurorin biyu na Majalisar Dokokin Isra’ila “Knesset” ta yi da su da nufin sanya kwace iko da mallakar yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gudanar da matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida ba bisa ka’ida ba.
Ma’aikatar ta ce a cikin wata sanarwa cewa: “Tana bayyana kakkausar suka da Iraki ta yi kan amincewar da Majalisar Dokokin Isra’ila ta yi da kudurorin biyu da nufin kwace iko da mallake yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma gudanar da gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna ba bisa ka’ida ba, matakin da ya zama keta dokokin kasa da kasa da kudurorin Majalisar Tsaro masu dacewa, da kuma take hakki kai tsaye na halaltattun hakkokin al’ummar Falasdinu.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iraki ta tabbatar da cewa “waɗannan matakan fadada suna lalata damar samun kwanciyar hankali da kuma ci gaba da tabbatar da mummunan kwace da mamaye yankunan da karfi, don wadannan matakai suna barazana ga tsaro da kwanciyar hankali a yankin baki daya,” tana mai jaddada “matsayinta mai karfi da goyon baya kan manufar Falasdinu da kuma ‘yancin al’ummar Falasdinu na neman ‘yancin kai da kuma kafa kasarsu mai cin gashin kanta, tare da kasancewar Qudus a matsayin babban birninta.”