Gaza: Jiragen Yakin HKI Sun Jefa Boma Bomai Kan Tentunan Yan Gudan hijiran Falasdinawa A Gaza

Jiragen yakin HKI sun yi luguden wuta kan tentunan yan gudun hijira Falasdinawa, a garin Khan Yunus na kudancin zirin Gaza, a ci gaba da

Jiragen yakin HKI sun yi luguden wuta kan tentunan yan gudun hijira Falasdinawa, a garin Khan Yunus na kudancin zirin Gaza, a ci gaba da keta hurumin yarjeniyar zaman lafiyan da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya jagoranta a ranar 10 ga watan Octoban shekara 2024.

Kamfanin dillancin labaran Iranpress na kasar Iran ya nakalto majiyar Falasdinawa a Khan  Yunus na cewa a safiyar jiya Talata ce, jiragen yahudawan suka kai hare hare  kan yankin inda suka kashe akalla mutane 8, a yayinda wasu da dama suka ji rauni.

Tun bayan tsagaita wutar yahudawan sun kashe falasdinawa akalla 1000 guda. Wannan bayan kissan kiyashi na mutane akalla 73,000 da raunata wasu fiye da 175,000. Daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted