Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa adadin ma’aikatan yada labarai da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 210 bayan kashe dan jarida Helmi al-Faqawi.
Al-Faqawi na cikin akalla mutane biyu da suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida kusa da wani asibiti a Khan Younis da sanyin safiyar ranar Litinin din nan.
Akalla mutane bakwai ne kuma suka jikkata a harin.
A cikin wani rahoto da aka buga a ranar 1 ga Afrilu, Cibiyar Watson ta ce yakin da Isra’ila ta yi a Gaza ya kasance mafi muni ga ma’aikatan yada labarai da aka yi rikodin kuma sojojin Isra’ila sun kashe ‘yan jarida 232 tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Hakan na nufin an kashe ‘yan jarida da yawa a Gaza fiye da yakin duniya na biyu, yakin Vietnam, yakin Yugoslavia da yakin Amurka a Afganistan.
A wani labarin kuma adadin wadanda suka mutu a Gaza tun soma yakin ya haura 50,700
Akalla mutane 57 ne aka kashe a Gaza a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yayin da 137 suka samu raunuka, kamar yadda ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya sanar.
Tun bayan da Isra’ila ta sake kai hare-hare a Gaza a ranar 18 ga Maris, adadin wadanda suka mutu ya kai 1,391, yayin da 3,434 suka jikkata.
Adadin wadanda aka kashe tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023 yanzu ya kai 50,752 yayin da wadanda aka jikkata ya kai 115,475.