Gamayyar Jam’iyyun Shi’a A Kasar Iraqi Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump Sun Goyi Bayan Maliki

Kungun jam’iyyun shia a kasar Iraki sun bayyana goyon bayansu ga Nuri Al-Maliki a matsayin firay ministan kasar duk tare da barazanar da shugaban kasar

Kungun jam’iyyun shia a kasar Iraki sun bayyana goyon bayansu ga Nuri Al-Maliki a matsayin firay ministan kasar duk tare da barazanar da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi na cewa zai dakatar da taimakon da Amurka take bawa kasar Iran mutanen Iraki sun sake zaben Maliki a karo na 3 Firay ministan kasar Iraki.

Bayanin da gungun jam’iyyun shia suka fitar ya nuna cewa batun zaben Firay minista al-amari na cikin gida ne kuma bai kamata wata kasa ta tsoma baki cikin sa ba.

Maliki dai wanda yake cikin jam’iyyar ‘Hizbul Daawa” ya sami amincewar Jam’iyyar na tsayawa takarar zama firay ministan kasar, kuma sauran jam’iyyun shia suka goya masa baya. Idan an gamasu gaba daya, suna da yawan da zasu kafa gwamnati tare da hadin kai da wasu jam’iyyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted