Shugaban kasar Kongo Yana Son A Cimma Zaman Lafiya Bayan Ya Sanya sharudda

Shugaban kasar DR Congo Félix chisekidi jim kadan bayan ganawa da tawagar sassanta rikici da kasar ke fama da shi da Rwanda,ya jaddada farin cikinsa da kuma fatan ganin an cimma zaman lafiya mai dorewa, duk da cewa ya shimfida  wasu sharudda a gaban  tawagar da kungiyar Afrika ta aike zuwa kasar. Félix Tshisekedi ya […]

IRGC Ya Musanta Cewa Sojojin Ruwa Na Amurka Sun Zo Yankin Ne Don Barazana Kawai

janar wahidi

Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya yi watsi da maganar cewa sojojin ruwa na Amurka sun zo yankin tekun farisa ne don yakin farfaganda, don haka dakarunsa a shirye suke su tunkari duk wani hari kan kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Burgedia Janar […]

An Yi Tattaunawa Ta Wayar Tarho Tsakanin Shugabannin Kasashen Iran Da Masar

A jiya Asabar da dare ne dai aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin shugabannin Iran Mas’ud Fizishkiyan da takwaran na kasar Masar Abdulfattah al-sisy akan halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya. Shugaban kasar ta Iran ya yi jinjina ga shugaban kasar Masar saboda kokarin da kasarsa take yin a […]