Shugabgan kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan wanda ya gana da fira ministan kasar Iraqi Muahmad Shiya Sudani a taron Doha na kasashen musulmi ya bayyana cewa; Wajibi ne kasashen musulmi su hada kai idan har suna son kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa.
Bugu da kari, shugaban kasar ta Iran ya kuma tattaunwa wasu hanyoyin da ya kamata a yi aiki da su, matukar ana son kawo karshen ta’addancin ‘yan sahayoniya.
Shugaba Fizishkiyan ya kuma ce, laifukan da HKI take tafkawa akan fararen hula a Gaza, da kashe yara da mata ta hanyar yunwa, wani lamari ne da hankali bai iya daukarsa, kuma idan musulmi su ka hada hannu da karfe wuri daya za su kawo karshensa.
A nashi gefen Fira ministan kasar Iraki ya bayyana abinda HKI take yi da cewa, isgili ne da dokokin kasa da kasa,don haka nauyi ne da ya doru a wuyan kasashen musulmi da su yi aiki domin ganin dukar matakan da suka dace.
Haka nan kuma ya ce, taron na birnin Doha dama ce ta daukar irin wadannan matakan.