Ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta sanar da cewa fira ministanta Ali Falih zai kawo ziyarar aiki na Iran a karshen makon da ake ciki, kuma kasashen biyu za su rattaba hannu akan yarjeniyoyi masu yawa.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen Iraki tana fada a jiya Lahadi cewa; Fira minista Ali Falih Zaidi zai ziyarci Iran a karshen mako, kuma idan ya zo kasashen biyu za su rattaba hannu akan yarjeniyoyi masu yawa da kuma na fahimtar juna akan fagagen ayyukan hadin gwiwa.
Kamfanin dillancin labarun na “Mehr” ya kuma ce; An yi ganawa a tsakanin jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a Iraki Muhammad Kazim ali-Sadiq da kuma babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Iraki, Muhammad Hussain Bahrul-Ulum a ma’aikatar harkokin wajen Iraki a birnin Bagadaza.
Bangarorin sun tattauna alakar kasashen nasu, da kuma jadawalin ziyarar da fira ministan na Irakin zai kawo Iran,haka nan kuma shirye-shiryen yadda ziyarar za ta kasance.
A nan birninTehran, jakadan Iraki a Iran, Yasir al-Hajjaj, ya ce wannan ce ziyarar farko da Fira minista Zaidi zai kawo zuwa Tehran, tare da jaddada cewa za ta taka rawa wajen bunkasa alakar kasashen biyu.
Haka nan kuma Hujjaj ya yi Ishara da yadda alaka mai zurfi take a tsakanin kashen biyu a tsawon tarihi, kuma za ta ci gaba da bunkasa.
Jakada Hujjaj ya kuma ce;manufar wannan ziyarar dai ita ce taka rawa wajen dawo da zaman lafiya da kawo karshen yaki a wannan yankin.