A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza.
Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi al-Faqawi da wani matashi mai suna Yousef al-Khazindar sun yi shahada, yayin da wasu ‘yan jarida da suka hada da Ahmed Mansour, Hassan Islayh, Ahmed al-Agha, Mohammed Fayek, Abdullah al-Attar, Ihab al-Bardini, Mahmoud Awad, da Majed Qudaih, suka samu raunuka a tashin bam din.
Kungiyar Kafafen Yada Labarai ta Falasdinu ta yi Allah wadai da wannan harin da Isra’ila ta kai a kan tantin ‘yan jarida a Khan Yunus, tare da nuna alhinin rasuwar dan jarida Hilmi al-Faqawi, wakilin tashar talabijin ta Falasdinu Alyaum.
Kisan dan jarida Ahmad Mansour ya janyo tofin Allah tsine daga kasashen Larabawa da ma duniya baki daya.
Kwamitin kasa da kasa da ke goyon bayan hakkin al’ummar Palasdinu ya yi tir da harin, inda ya bayyana shi a matsayin laifin yaki da nufin rufe bakin ‘yan jaridu tare da dakile bayanan cin zarafin da Isra’ila ke yi a Gaza.
Masu fafutuka na kafofin watsa labarun sun kuma nuna rashin jin dadi, suna nuna yadda Isra’ila ke ci gaba da cin zarafin ɗan adam-musamman a kan ‘yan jarida, waɗdanda ke da hakkin samun kariya a karkashin dokar jin kai ta duniya. A cewar ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza, adadin ‘yan jaridar da aka kashe tun ranar 7 ga watan Oktoba 2023 ya zarce 210.