Search
Close this search box.

Dakarun Kai Daukin Gaggawa A Sudan Sun Kai Hari Kan Masallaci Tare Da Kashe Mutane 28

Mayakan dakarun kai daukin gaggawa sun kashe fararen hula 28 a wani hari da suka kai birnin El- Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa

Mayakan dakarun kai daukin gaggawa sun kashe fararen hula 28 a wani hari da suka kai birnin El- Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa

Gwamnan jihar Darfur ta Arewa da ke yammacin kasar Sudan, Al-Hafiz Bakhit, ya sanar da cewa, an kashe fararen hula 28 tare da raunata wasu 46 na daban a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai a birnin El-Fasher, a lokacin da jama’asuke gudanar da sallar Asuba.

Bakhit ya kara da cewa: Sojojin Sudan da dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin masu dauke da makamai da suke tallafawa sojojin kasar sun mayar da martani kan dakarun kai daukingaggawa, inda suka gwabza fada har na tsawon sa’o’I 10 a tsakaninsu a birnin na El-Fasher.

Gwamnan ya kara da cewa: Sun yi takaicin ganin yadda kungiyar Rapid Support Forces take kashe ‘yan Sudan kuma fararen hula wasu a gidajensu yayin da a halin yanzu har a Masallaci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments