Cutar Kwalara Ta Yadu A Sudan Baya Ga Matsalar Tashe-Tashen Hankulan Da Suke Ci Gaba Da Yuduwa A Kasar

Cutar kwalara ta yadu a Sudan, kuma ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan asibitoci biyu a Jihar El Obeid na kasar

Cutar kwalara ta yadu a Sudan, kuma ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan asibitoci biyu a Jihar El Obeid na kasar

Sudan na ci gaba da fama da tabarbarewar yanayin tsaro da lafiya bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan. A bangaren tsaro kuma, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces sun kai hare-haren bama-bamai a wasu asibitoci biyu da wasu unguwanni a birnin El Obeid da ke Arewacin Kordofan a tsakiyar kasar Sudan.

Wata majiyar soji ta bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa sun afkawa Asibitin Al-Daman da kuma Jami’an lafiya da ke tsakiyar birnin da manyan bindigogi.

Sojojin Sudan sun tabbatar da cewa: Sun yi luguden wuta kan sansanonin dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da ke arewacin jihar Kordofan da makaman atilare, yayin da dakarun kai daukin gaggawar suka yi nuni da cewa; sun kwace iko da yankunan Al-Hamadi da Kazgil da ke kudancin birnin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments