Cuba Ta  Ayyana Zaman Makoki Na Kwanaki Biyu Saboda ‘Yan Kasarta 32 Da Amurka Ta Kashe A Harin Venezuela

Gwamnatin kasar Cuba ta sanar da cewa ‘yan kasarta da Amurka ta kashe a Venezuela,dukkaninsu ma’aikatan ma’aikatar harkokin cikin gida ne da kuma dakarun juyin

Gwamnatin kasar Cuba ta sanar da cewa ‘yan kasarta da Amurka ta kashe a Venezuela,dukkaninsu ma’aikatan ma’aikatar harkokin cikin gida ne da kuma dakarun juyin juya halin kasar. Haka nan kuma sanarwar ta kara da cewa, an tura mutanan ne zuwa Venezuela bisa bukatar gwamnatin kasar.

Sanarwar ta ce, “A sakamakon harin ta’addanci da Amurka ta kai wa jamhuriyar Venezuela, mun yi Rashin mutane 32 a cikin halin yaki.”

Haka nan kuma bayanin ya ci gaba da cewa, mutanen sun rasa rayukansu ne a cikin jarunta a yayin da suke aiwatar da nauyin da ya rataya a wuyansu, kuma gumurzu su ka yi sosai da masu wuce gona da iri da su ka kai hari.”

Shugaban kasar ta Cuba Miguel Díaz-Canelya rubuta a shafinsa na X cewa: “Daukaka ta tabata ga mayakan Cuba,wadanda su ka kwanta dama wajen kalubalantar ‘yan ta’adda da suka nada kansu shugabannin duniya.”

Da akwai alaka mai karfi a tsakanin kasashen Cuba da Venezuela tun a shekarun 1990’ da kuma lokacin da Hugo Chaves ya zama shugaban kasa,wacce kuma take ci gaba har zuwa yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted