Bloomberg: FBI ta cire sunan Trump daga Fayilolin badakalar Epstein

Bloomberg, ya nakalto wasu majiyoyi uku da ba a bayyana sunansu ba, sun ruwaito cewa, hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI) ta sauya

Bloomberg, ya nakalto wasu majiyoyi uku da ba a bayyana sunansu ba, sun ruwaito cewa, hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI) ta sauya sunan shugaban Amurka na yanzu Donald Trump da wasu manyan mutane daga takardun gwamnati da suka shafi shari’ar marigayi mai kudi Jeffrey Epstein.

Hukumar ta bayyana cewa sun yanke shawarar sauya sunayen da suka hada da na Trump ne saboda matsayinsu na ‘yan kasa a lokacin da aka fara gudanar da bincike a shekarar 2006, inda ta ce bayyanar sunayen mutane a irin wadannan fayiloli ba wai yana nufin suna da hannu cikin wani laifi ba.

An kama Epstein a cikin 2019 kuma an tuhume shi da laifin safarar yara kanana don yin lalata, laifin da ke da hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari, baya ga tuhumar hada baki, wanda zai iya kai shekaru biyar.

Epstein ya mutu ne a cikin dakinsa makonni bayan kama shi, lamarin da ya haifar da cece-kuce game da yanayin mutuwarsa da yiwuwar alakarsa da fitattun masu siyasa da tattalin arziki a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments