Premium-Masana sun tabbatar da cewa za a iya shawo kan kashi 80% bisa 100% na yawan kisan da cututtukan da suka jiɓinci matsalolin zuciya (CVD) ta hanyar mutum ya sauya tsarin yadda yake tafiyar da rayuwar sa.
Shugaban Ƙungiyar Likitocin Kula da Ciwon Zuciya na Najeriya, Farfesa Augustine Odili, ya ce sama da mutum miliyan 20.5 ne ke mutuwa sanadiyyar cututtukan da ke da nasaba da matsalolin zuciya duk shekara a duniya.
Odili ya yi gargaɗin cewa kashi 75% daga cikin mutum miliyan 20.5 ɗin kuma su na mutuwa ne a ƙasashen da al’umma ba su da ƙarfin arziki da waɗanda ke ci da kyar, sha ma da kyar.
Farfesa Odili wanda ƙwararren masanin cututtukan da suka shafi zuciya ne, ya yi wannan bayani cikin wata sanarwar da aka fitar wa manema labarai a ranar Lahadi, a shirye-shiryen zagayowar Ranar Masu Cutar Zuciya ta Duniya, ta 2024.
Ya ce an ware wannan rana ce domin a zaburar da kuma tashi a ƙara azamar shawo kan gagarimar illar da cututtukan zuciya ke haifawa.
Ya ce ƙungiyar su za ta shekara biyu cur ta na kamfen na ƙoƙarin daƙile yawan mace-macen da zutar zuciya ke haddasawa, daga nan har zuwa 2026.
Ya ce hakan na nufin a riƙa goya mutane baya domin su kula da zuciyar su, tare da jan hankalin shugabanni su ɗauki matsalar ciwon zuciya da muhimmanci sosai.