Baqa’i: Amurka Abokiyar Zaluncin ‘Yan Sahayoniyya Ne

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Amurka abokiyar tarayya ce a dukkan laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke aikatawa a Lebanon, Falasdinu da

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Amurka abokiyar tarayya ce a dukkan laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke aikatawa a Lebanon, Falasdinu da kuma yankin baki daya

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da mummunan hare-haren da ‘yan sahayoniyya suka kaddamar a ‘yan kwanakin nan kan yankunan kudancin Lebanon, wanda ya yi sanadiyyar shahada da raunata wasu ‘yan kasar Lebanon da kuma lalata kayayyakin more rayuwa da gidajen fararen hula.

Da yake nuni da ci gaba da hare-haren da ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa da kuma keta ‘yancin kasar Lebanon da kuma cikakken ikon mallakar yankunan kasar, Baqa’i ya bayyana cewa shiru da rashin kulawa da al’ummar duniya ke yi – musamman Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya – ya kara wa ‘yan sahayoniyya kwarin gwiwa, wanda hakan ya haifar da ci gaba da kai hare-hare da tafka muggan laifuka.

Ya jaddada cewa gwamnatin Amurka mai ci a yanzu, sakamakon cikakken goyon bayan da take bai wa wannan gwamnati ‘yar mamaya, tana da hannu tare da goyon baya ga dukkan laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take aikatawa a Lebanon, da Falastinu da aka mamaye da kuma daukacin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted