Bankin Duniya : Sake Gina Lebanon Yana Bukatar Dala Biliyan 11

Bakin duniya ya kiyasta cewa ana bukatar dala biliyan 11, domin sake gina Lebanon sakamakon barnar da hare haren Isra’ila suka haifarwa kasar. Bangaren gidaje

Bakin duniya ya kiyasta cewa ana bukatar dala biliyan 11, domin sake gina Lebanon sakamakon barnar da hare haren Isra’ila suka haifarwa kasar.

Bangaren gidaje na Lebanon ya fi fama da matsalar, inda aka kiyasta asarar da ta kai dala biliyan 4.6, yayin da masana’antar yawon bude ido ta yi asarar dala biliyan 3.6.

“Sakamakon rikice-rikicen ya haifar da raguwa a ainihin GDP na Lebanon na 7.1 bisa dari a 2024,” in ji Bankin Duniya.

Rahoton ya kara da cewa, “Ya zuwa karshen shekarar 2024, raguwar GDP na kasar Lebanon tun daga shekarar 2019 ya kusan kashi 40%, wanda hakan ya haifar da koma bayan tattalin arziki a bangarori da dama da kuma yin tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar.”

Sojojin Isra’ila sun fara kai farmaki kan sansanonin Hizbullah a kudancin Lebanon jim kadan bayan kaddamar da kisan kiyashi a zirin Gaza da aka yiwa kawanya a watan Oktoban shekarar 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments