Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula.
A cikin wani jawabi kai tsaye ta gidan talabijin, Al-Hayya ya bayyana cewa: “Ya ku ‘ya’yan Dakarun Qassam, da na Quds Brigade, da kuma sauran kungiyoyin gwagwarmaya, abin da kuke yi ya kawo cikas ga farmakin da motoci masu sulke na makiya suke yi.
Khalil ya jaddada cewa: Babban hafsan hafsoshin sojin makiya yana rufe gazawar sojojinsa da kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hulan Falasdinawa.