ASUU-KASU A Kaduna Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

ASUU-KASU ta yi barazanar shiga yajin aiki bayan gwamnatin Jihar Kaduna ta kasa aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da kungiyar tun a shekarar 2025.

Kungiyar malaman jami’o’ii na Najerira reshen jami’ar kaduna ASSU-KASU ta yi bara zaranar shiga yakin aiki na sai baba ya gani bayan da gwamnatin jihar ta kasa aiwatar da yarjeniyar da aka cimma da gwamnati a shekara ta 2025.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto shugaban ASSU-KASU Dr Abubakar Abdullahi yana fadar haka a wani taron kafafen yada labarai da ya kira a ranar Litinin a kaduna. Ya kuma kara da cewa rashin aiwatar da yrejeniyar da aka cimma da gwamnatin tarayyar kasar wanda yakamata ya fara a farkon shekara ta 2026 ya sa malamai a jami’ar kaduna kimani 200 suka bar aiki a jami’ar da dama sun sami ayyuka a wasu jami’o’ii a ciki ko wajen jihar.

Abdullahi ya kara da cewa, a halin yanzu sun bawa gwamnatin tarayyar makonni biyu su aiwatar da alkawalin da aka cimma da su, ko kuma su fara yajin aiki na sai babata ta gani.

Shugaban ASSU-KASU ya kara da cewa sun sha tunatar da hukumomin da abin yashafa dangene da halin da ake ciki, wadanda suka hada da hukumar Jami;o;iii ta kasa, da Gwamna Uba Sani wanda ya kawo ziyara ganin ido a Jami’ar, amma babu abinda ya faru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted