Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Bullar Fari a Kudu maso Yammacin Asiya yana ba da dama don ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashe maƙwabta
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Fari da ke fuskantar Kudu maso Yammacin Asiya zai iya mayar da shi dama ta ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.
Kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA ya ruwaito cewa: Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin da ya kai ziyara a safiyar Juma’a a cibiyar gudanarwa da kula da kamfanin ruwa da sharar gida da ke birnin Mashhad mai alfarma da ke gabashin Iran.
A lokacin ziyarar, Araqchi ya ce: “Bisa ga hasashen yanayi game da yankin, Kudu maso Yammacin Asiya na fuskantar fari. Baya ga kula da samar da ruwa da amfani da shi, za a iya mayar da wannan yanki na haɗin gwiwa da maƙwabtan Iran.”
A farkon ziyarar, Shugaban Kamfanin Ruwa da Sharar Gida na Mashhad, Isma’iliyan, ya gabatar da taƙaitaccen bayani game da matakan da aka aiwatar a cikin ‘yan shekarun nan don tabbatar da ruwa da kuma sarrafa amfani da shi a Babban Mashhad a ƙarƙashin yanayin fari da ke ci gaba da faruwa.