Iran ta sake nanata matsayinta na kin shiga shawarwari kai tsaye da Amurka kan shirinta na nukiliya, maimakon haka ta bukaci a ci gaba da shawarwarin ta hanyar masu shiga tsakani.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya bayyana hakan, yana mai cewa babu wata tattaunawa da aka da Washington, kuma ba za a yi irin wannan tattaunawa ba sai dai ta hanyar masu shiga tsakani.
“Mun bayyana matsayinmu, muna goyon bayan bin hanyoyi na diflomasiyya da tattaunawa, amma ta hanyar masu shiga tsakani. Tabbas, ba a gudanar da wata tattaunawa kai tsaye tsakanin Iran da Amurka ba, ” in ji Araghchi a cikin wata sanarwa da ya fitar a dandalin Telegram.
Kalaman nasa sun zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan ta ki amincewa da kulla wata sabuwar yarjejeniya kan shirinta na nukiliya.
Araqchi yace, Iran ba zata taba yarda da duk wani mataki na shigo-shigo ba zurfi ba, domin kuwa irin wannan ne aka yi wa kasar Libya, a lokacin da ta yi watsa da shirinta na nukiliya kuma aka ci gaba da kakaba mata takunkumai, daga karshe kuma kasashen turai da kungiyar tsaro ta NATO suka hambarar da gwamnatin kasar a lokacin mulkin Ghaddafi.