Arakci: Amurka Tana Mafarkin Kulla Yarjejeniya Da Iran Kwatankwanci Wacce Ta Yi Da Kasar Libya

Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba

Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba.

Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban  kwamitin siyasar waje na majalisar shawarar musulunci ta Iran ya gabatar da rahoto akan hali na karshe da ake ciki dangane da batun tattaunawa da Amurka.

Arakci ya kuma fadawa kwamitin cewa; Mu ma’abota diflomasiyya da tattaunawa ne, amma za mu tattauna da Amurka ne ba kai tsaye ba,kuma duk da hakan ma har yanzu ba mu bude tattaunawar ba.”

Wani daga cikin ‘yan kwamitin ya tambayi Arakci akan ko Amurka tana tunanin kulla yarjejeniya da Iran irin wacce ta yi da Libya a 2003?

Arakci ya ba shi jawabi da cewa; Abu ne mai yiyuwa mafarkin da suke yi kenan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments