Fira ministan yankin na Greenland wanda yake a cikin kasar Holland ya fada wa shugaban kasar Amurka cewa; Abinda yake yi ya isa haka.”
Fira ministan yankin na Greenland ya rubuta a shafinsa na “facebook” cewa; Ba ma son a ci gaba da yi mana matsin lamba, ko kuma yi mana shagube,balla kuma yin mafarkin tsaye na hade Greenland da kasar Amurka.”
Sai dai Fira ministan na Greenland ya ce a shirye suke a bude tattaunawa, amma ta kasance ta hanyar da ta dace, kuma bisa dacewa da dokokin kasa da kasa.
Shi kuwa fira ministan kasar Birtaniya Keir Starmer cewa ya yi, London tana goyon bayan Danmark kuma muna tare da fira ministar kasar ,akan hakkin ayyana makomar Greenland.”
Haka nan kuma ya ce, yankin Greenland da kuma masarautar Danmark ne suke da hakkin ayyana makokar yankin na Greenland.
A can kasar Faransa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje Pascal Confavreux ya fadawa Tv1 cewa babu yadda za a sauya iyakokin kasashe ta hanyar amfani da karfi.
Ita ma kasar Chana ta yi kira ga Amurka da ta daina yi wa China barazana a matsayin wani dalilin fakewa don cimma manufa.”
Kasar Finland kuwa ta bakin shugabanta, Alaxender Stub, ya ce; “ Ba wani zai iya ayyanawa Greenland makoma, sai ita kanta da kuma kasar Danmark.
Trump ya furta cewa, muna da bukatar yankin Greenland saboda dalilai na tsaron kasa, ita kuwa kasar Danmark ba za ta taba yi mana hakan ba.”
Trump ya kuma ce, daga nan zuwa watanni biyu, ko kuma kwanaki ashirin za mu yi tunanin abinda ya kamata mu yi akan Greenland.