Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as.
Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara 40.
Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci.
Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci da kuma girmama jama’a, wadanda suka girme shi da ma wadanda ya girma.
Allah madaukain sarki ya aiko da sako zuwa ga bil adama, wanda ya zama sanadin shiririyar jama’a da dama a lokacinsa, mafi yawan wadanda suka muslunta tare da manzon Allah a Makka sun musulunta ne sakamakon kyawawan dabi’unsa, kamar yadda da dama daga cikin wadanda suka muslunta a Madiana bayan hijira sun karbi muslunci ne sakamakon kyawawan dabi’u da suka gani tare da manzon Allah, wadanda addinin ke koyar da dan Adam.