Ana Babban Zabe A Afrika Ta Kudu

A Afrika ta Kudu yau Laraba ne al’ummar kasar ke kada kuri’a a babban zaben kasar inda zasu zabi ‘yan majalisar dokokin da zasu zabi

A Afrika ta Kudu yau Laraba ne al’ummar kasar ke kada kuri’a a babban zaben kasar inda zasu zabi ‘yan majalisar dokokin da zasu zabi shugaban kasa da mashawartansa na jihohi a nan gaba.

Kimanin ‘yan Afirka ta Kudu miliyan 27.6 ne aka tantance domin kada kuri’a.

matsalar rashin aikin yi da cin hanci da rashawa da kuma katsewar ruwa da wutar lantarki, su ne babban kalubale dake gaban jam’iyyar ANC da ke mulki tun 1994.

An bayyana zaben da mai cike da tarihi idan jam’iyyar ANC, ta rasa rinyaje a fadin kasar, wanda hakan zai kasance karo na farko  a cikin shekaru 30, bayan zaben demokuradiyya na farko wanda ya kawo Nelson Mandela kan karagar mulki.

A jimilce jam’iyyu 52 ne ke fafata neman kujeru 400 na ‘yan majalisar dokoki.

Jam’iyyar ANC, dake mulki tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata, a shekarar 1994, na cikin tsaka mai wuya.

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a a baya-bayan nan ta nuna cewa jam’iyyar ANC zata samu kashi 40 zuwa 45 na kuri’un da aka kada, kasa da kashi 50%.

A zaben 2019 jam’iyyar ta samu kashi 57,5% ne.  

Sauren manyan jam’iyyun da zata fafata dasu a wannan zaben sun hada da DA, EFF Da MK.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments