An sake zanga-zangar kin jinin gwamnatin Netanyahu a Tel-Aviv

A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista

A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington.

Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun yi Allah wadai da manufofin Netanyahu, ciki har da yunkurinsa na korar manyan jami’an tsaro da na shari’a na gwamnatin.

Sun kuma yi Allah wadai da sake dawo da yakin kisan kare dangi da ake yi wa al’ummar Gaza.

Iyalan ‘yan Isra’ilar da aka yi garkuwa da su a Gaza su ma sun shiga zanga-zangar, inda suka bukaci a kawo karshen yakin da kuma kulla yarjejeniyar tabbatar da sakin mutanen da aka kama.

Kungiyar dai ta ce za ta saki sauran mutanen da ake garkuwa da su ne kawai idan an sako sauren fursunonin Falasdinawa da Isra’ila ke rike da a gidajen yarinta, da kuma tabbatar da tsagaita bude wuta, da kuma janyewar Isra’ila gaba daya daga Gaza.

A ranar 18 ga watan Maris da ya gabata ne, Isra’ila ta sake kaddamar hari a Gaza wanda ya keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan Janairu, inda ta kai hare-haren wuce gona da iri tare da kashe daruruwan Falasdinawa, ciki har da yara sama da 100.

Tun daga wannan lokacin, adadin wadanda suka mutu ya kai 1,391, yayin da wasu 3,434 suka jikkata, a cewar majiyoyin lafiya na Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments