A sabbin bayanan da suke fitowa dangane da yarjeniyar mamayar kasar Lebanon wanda Gwamnatin kasar da kuma HKI zasu yi, ya nuna cewa da farko sojojin kasar Lebanon ne zasu aiwatar da shirin, inda zasu shiga duk inda dakarun Hizbullah suke a kudancin kasar, su fiddasu sannan sojojin HKI suna janye daga kasar a hankali a hankali, idan ikon yankin ya sake komawa hannun gwamnatin kasar. HKI zata sake dawowa da kwace kasar tunda sojojin kasar Lebanon ba zasu iya hana su yin haka.
Amma kungiyar Hizbullah ta ki amincewa da wannan shirin, ta kuma bayyana cewa tana tare da shirin Iran na yarjeniyar Switzeeland ta ficewa sojojin mamaya daga kudancin kasar Lebanon bayan dakatar da budewa juna wuta.
Hakama kakakin majalisar dokokin kasar Lebanon Nabi Berri ya sha al-washin hana shirin Amurka da HKI da kuma gwamnatin kasar Lebanon na kwance damarar kungiyar hizbullah.