Rahotanni sun bayyana cewa yan sanda a isra’ila sun kama wasu yahudawa yan share wuri zauna su hudu bayan da suka kai hari kan motocin dake dauke da ma’akatan gidan talabijin na CNN tare da yin raga-raga da motarsu a yankuna da aka mamaye a gabar yammacin kogin jodan
Dan rahoton gidan talabijin na CNN ya bayyana cewa yahudawa yan share wuri zauna sun kai hari kan tawagar yan jaridu a lokacin da suke wucewa ta Ramallah, hedkwatar mulki ta falasdinu, yan jaridar suna rahoto ne a kauyen sinjil dake arewacin ramallah lokacin da aka kai musu harin,
Rahoton da aka yada a shafin yanar gizo ya nuna cewa yahudawa yan share wurin zauna sun tare hanya tare da hana motoci wucewa ta wajen,
Haka zalika ya ce sau 3488 yahudawa yan share wurin zauna suka kai hari a gabar yammcin kogin Jodan a rabin wannan shekarar, kuma yayi sanadiyar mutuwar falasdinawa17, hukumar kare hakkin bil adama ta bayyana cewa Isa’ila ce ta bawa yahudawan damar aikata duk wani laifi kan falasdinawa.