Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa, an dage taron kasashen larabawa na yankin tekun farisa a birnin Mascat na kasar Omma, wanda ake shirya gudanar da shi a yau litinin, tare da bukatar daya daga cikin kasashen.
Kamfanin dillancin labaran IRNa na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar tana tabbatar da labarin a jiya Lahadi.
Mohammad Ali Bak darakta mai kula da al-amuran kasashen larabawa na yankin tekun farisa a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran ya bayyana cewa an dauki shawarar dage taron ne bayan wata tattaunawa tsakanin Iran da Omman da kuma tare da bukatar wasu kasashen yankin.
A yau litinin ce yakamata a gudanar da taron, amma an ga yakamata a jinkirtashi saboda wasu dalilai masu muhimmanci inji Bak.
Ya ce kasashen Iran da Omman zasu yi nazarin wani lokaci da ya dace, nan gaba don gudanar da taron. Banda haka Ministan harkokin wajen kasar Omman ya bada sanarwan cewa an dage taron ministocin harkokin waje na kasashen larabawa na yankin tekun farisa zuwa wani lokaci.