Washington ta fitar da rahoton cewa ta aike da sako ga gunguna yan shia masu rinjaye a majalisa cewa za su fuskanci mummunan takunkumi Amurka kan muhimman wurare a kasar idan suka sanar da sunan Nuri al-maliki a matsayin sabon fira ministan kasar na gaba.
yace kasar Amurka ta yi barazanar kakaba takunkumi kan babbar hukumar dake kula da harkokin mai a kasar, da kuma babban bankin Iraki, da sauran bangarorin tsaro da na diflomasiya, da kuma manyan jami’an siyasa tsoffi da kuma na yanzu.
shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadi cewa kasar Amurka tana mayar da hankali sosai kan batutuwan da suka shafi zaben Nuri al’maliki a mukamin fira ministan kasar Iraqi.
A farkon wannan watan Nuri Maliki yace janyewarsa daga takarar shugabancin zai kawo cikas ga ikon mulkin Iraki, yana mai jaddada cewa zai sauka ne kawai idan hadakar yan shia suka bukaci haka.