Kasar Habasha Ta Girke Dakaru A Tigray Saboda Fargabar Barkewar Yaki Tsakani

Gwamnatin Habasha ta sanar da girke dakaru akan iyakar yankin Tigray ta arewaci a wani yanayi da majiyoyin diflomasiyyar yammacin duniya ke ganin akwai yiwuwar barkewar sabon yaki tsakanin dakarun kasar ta gabashin Afrika da yan tawayen yankin. Wasu majiyoyi sun ce sojojin na Habasha yanzu haka na kokarin yiwa yankin Tigray kawanya inda a […]

Araqchi: An Samun Ci Gaba Sosai A  Tattaunawar Da Suka Yi Da Amurka A Ganeva

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar cewa tattaunawa zagaye ta biyu da aka yi ba ta kai tsaye ba da Amurka kan batun cire mata takunkumi an cimma yarjejeniyar kan wasu ka’idoji da za su jagoranci wadanda za su daidaita tattauna ta gaba don cimma yarjejeniya mai karfi.           Da yake […]

Yan Sanda Isra’ila Sun Zafafa Kai Hare-hare A Masallacin Qudus

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an yan sanda HKI sun tsananta kai hare-hare a masallacin Qudus kuma zai ci gaba a tsawon wata guda na Azumin watan Ramadan kamar yadda gwamnatin sahyuniya ta sanar da fara tsananta bincike a harabar masallacin. Arad Braverman wani babban jami’in yan sandan isra’ila a birnin kudus yace zaa baza jami’an […]

Kasashen Nijar Da Aljeriya Sun Sanar Da Bude Sabon Shafi A Cikin Alakarsu

Shugaban mulkin soja na jamhuiryar Nijar, Janar Abdurrahman Tiani wanda ya kai ziyarar aiki kasar Aljeriya ya sanar da bude sabon shafi a alaka da kasar. Janar Abdurrahman Tiani ya gana da takwaransa na kasar Aljeriya, Abdulmajid Tebbani a birnin Alges a jiya Litinin inda su ka tattaunawa batun shimfida bututun iskar Gas. A nashi […]

 Geneva: A Yau Talata Za A Fara Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka A Birnin Geneva

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto wata majiya ta kusa tana cewa; Da tsakiyar ranar yau ne za a bude tattaunawar  Nukiliya a tsakanin tawagogin Iran da na Amurka a birnin Geneva na kasar Switzerland ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman. Tattaunawar ta yau ita ce zango na biyu a tsakanin bangarorin biyu, bayan wacce […]

Iran Ta Soki Gwamnatin Kasar Amurka Kan Kara Takurawa Kasar Cuba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya tir da gwamnatin kasar Amurka kan kara takurawa gwamnatin kasar Cuba da take yi, bayan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar shekaru fiye da 60 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Esmail Baghaei kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yana fadar […]

Iran: Rundunar IRGC Sun Fara Atisayen Soje A Mashigar Ruwa Ta Hurmuz

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran wata IRGC rashen sojojin ruwa sun fara atisayen soje wanda suka bawa suna sarrafa mashigar ruwa na Hurmuz tare da amfani da kayakin zamani. Labarin ya kara da cewa Manjo Janar Mohammad Pakpoour babban kwamandan rundunar reshen sojojin ruwa ne ya ke sanya ido a kan […]

Jirage Marasa Matuka Sun Kashe Mutane Akalla 28 A Sudan

Kungiyoyin kare hakkin bi’adama a kasar Sudan Sun bayyana cewa makaman Drones wadanda dakarun RSF suka cilla sun kashe mutane akalla 28 a cikin wata kasuwa a yankin Kordofan. Shafin yanar gizo na labarai Arab news ya bayyana cewa makaman sun fada kan kasuwar Al-safiya da ke garin Sodari a lardin areawacin Kordofan a ranar […]