Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare kan Yemen

Amurka na ci gaba da kai hare-hare kan Yemen, inda ta kai sabbin hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na kasar a baya bayan nan.

Amurka na ci gaba da kai hare-hare kan Yemen, inda ta kai sabbin hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na kasar a baya bayan nan.

Kafar yada labaran kasar Yemen ta bayyana cewa, Amurka ta kai akalla hare-haren jiragen yaki guda uku a gundumar Bani Matar da ke lardin Sanaa.

Akalla fararen hula hudu ne suka mutu sannan wasu 25 suka jikkata, ciki har da mata 11 da yaro daya.

Hakazalika jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare guda hudu a tsibirin Kamaran da ke al-Hudaydah a yammacin kasar Yemen.

Wasu hare-hare uku na Amurka sun kai hari a lardin Hajjah da ke yammacin kasar Yemen.

Amurka da kawayenta sun zafafa kai hare-hare kan kasar Yemen bayan da ta koma yaki da Isra’ila sakamakon sabon kisan kiyashi da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza.

Galibin hare-haren da Amurka ke kaiwa kan gine-ginen fararen hula ne, lamarin da ke haddasa mace-mace da jikkata a tsakanin jama’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments