Shugaban jam’iyyar ‘Hikimah Ta Kasa’ Ammar Hakim ta kasar Iraki, ya gana da shugaban dakarun Hashdu Ashabi na kasar ta Iraki inda suka tattauna al-amuran tsaron kasar Iraki da kuma harkokin tsaro a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Sahab na kasar Iran ya bayyana cewa shugabannin biyu sun bayyana bukatar kiyaye rundunar Hashdushabi, don muhimmansu wajen kare kasar daga duk wani hatsari.
Jami’an guda biyu sun kara jaddada bukatar kasancewar dakarun Hashdu cikin cibiyoyin tsaro masu muhimmanci a kasar ta Iraki don irin sabikan da suke da shin a yakar kungiyar yanta’adda ta Daesh a shekarum bayan.