Rahotanni sun bayyana cewa Ammar Al-hakeem shugaban kungiyar national wisdom movement ya gana da shugaban majalisar koli ta tsaron kasa Ali larijani a nan birnin Tehran inda suka tattauna kan hanyoyin da zaa bi wajen kara danko zumunci da kuma yin aiki tare da kuma samar da tsaro a yankin,
Sayyed Hakeem ya kawo ziyarar aiki ne a nan kasar Iran inda zai tattauna da jami’an gwamnati kan dangantakar dake tsakaninsu da kuma ci gaban yankin da kuma yadda za su hada kai wajen inganta tsaro da zaman lafiya,
A lokacin ganawar dukkan bangarorin biyu sun yi nuni game da muhimmanci dabaru da hadin guiwa da kuma yin aiki tare , kana yayi ishara game da muhimmanci hadin kai kasashen biyu yadda zasu yi aiki tare wajen tunkarar kalubalan dake gabansu a yankin, kana ya mika sakon girmamawa ga wanda ya assasa juyin musulunci a iran imam khomaini yardar Allah ta tabbata gare shi.