Zanga-zangar al’umma da aka yi a kasar Iraki ta yi Allah wadai da dakatar da jigilar jiragen sama na Iran
‘Yan Iraki sun yi zanga-zanga a larduna da dama na kasar a ranar Litinin don nuna rashin amincewarsu da dakatar da zirga-zirgar jiragen saman Iran zuwa kasar.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa: ‘Yan kasar Iraki sun taru a gaban filin jirgin saman birnin Najaf don amsa kiran da kungiyar “Al-Nujaba ta Iraki” ta yi, suna masu jaddada adawa da shawarar dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Iran.
Rahotannin sun nuna cewa: Dimbin jama’a sun taru a filin jirgin saman don nuna rashin amincewarsu da shawarar da hukumomi suka yanke na dakatar da jiragen saman Iran.
Birnin Karbala ya kuma fuskanci zanga-zanga a ranar Litinin kan dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Iran – wani mataki da aka ruwaito cewa: Amurka ce ta shirya wannan makirci – inda aka bayyana matakin a matsayin keta hurumin kasar Iraki.