Al-Houthi: Mun Ba Wa Isra’ila Wa’adin Kwanaki 4 Da Ta Kawo Karshen Killace Gaza

Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin

Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila.

A cikin wani jawabi da ya yi wanda aka watsa a gidajen talabijin na ciki da wajen kasar Yemen, Al-Houthi ya soki ta’annutin da  Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinu, yana mai jaddada cewa, rashin aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma hana shigar da kayan agaji a Gaza da kuma ci gaba da killace yankin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi, lamari ne mai matukar hadari.

Al-Houthi ya zargi Isra’ila da kin yin aiki da alkawuran da ta dauka a karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a kan Gaza, musamman dangane da ayyukan jin kai, yana mai cewa Hamas ta cika dukkanin alkawullanta da kuma sauke nauyin da ya rataya a wuyanta, ta hanyar kiyaye wannan  yarjejeniyar.

Har ila yau Al-Houthi ya yi Allah wadai da zafafa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a yankunan yammacin gabar kogin Jordan da kuma al-Quds, yana mai bayyana irin rawar da Isra’ila ke takawa wajen kara kai hare-hare kan Falasdinawa a matsayin laifin yaki.

Baya ga haka kuma, Ya soki yadda Amurka ke goyon bayan mamayar Isra’ila ido rufe a karkashin Shugaba Donald Trump, yana mai cewa goyon bayan Washington ya karfafa gwiwar Isra’ila wajen ci gaba da muzgunawa Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments