Shugaban Rundunar sa kai ta al’ummar kasar Iraki wato Hashd Al Shaabi (PMF) Faleh al-Fayadh, ya tabbatar da cewa, dakarun Iraqi Popular Mobilisation Forces (PMF) suna kare Iraki ne kawai kuma ba su da wata rawar da suke takawa a wajen kasar Iraki.
A yayin wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin, al-Fayadh ya tabbatar da cewa ‘yan Iraki ne suka rubuta dokar ta Popular Mobilisation Forces (PMF) tare da halartar masana shari’a da kwararru daga ma’aikatar tsaro, tare da musanta duk wani tsoma bakin kasashen waje wajen tsara ayyukan rundunar.
Ya kara da cewa, “Akwai jam’iyyun da ke kawo cikas wajen amincewa da dokar da ake shiryawa a yanzu,” yana mai cewa hukumar ba ta da hurumin yin katsalandan a cikin majalisa da kuma dokokinta, amma suna fatan za a gaggauta amincewa da dokar.
Al-Fayadh ya ce, har yanzu akwai bukatar ayyukan wadannan dakaru na sa kai, tare da jaddada cewa al’amuran yankin ba su yi muni kamar shekarar 2014, lokacin da aka kafa PMF domin kare kasar ba, wannan kuwa sakamako na jajircewa da sadaukarwa ta wadannan dakaru tare da hadin gwiwa da sauran bangarorin tsaro na kasa.
Al-Fayadh ya kuma jaddada cewa, Popular Mobilization Forces (PMF) suna amsar umarni ne kawai daga babban kwamandan sojojin kasar.
Shugaban na PMF ya yi ishara da cewa dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran karkashin jagorancin shahid Qassem Soleimani sun taimaka wa Iraki wajen kare kanta daga barazanar ta’addanci.