Admiral Irani: Ba da jimawa ba, Iran Za Ta Fito Da Makamin Da Zai Firgita Abokan Gaba

Babban kwamandan sojan ruwan jamhuriyar musulunci ta Iran Admiral Shahram Irani, ya bayyana cewa, A halin yanzu Iran tana kara karfafa makamanta kuma da  izinin

Babban kwamandan sojan ruwan jamhuriyar musulunci ta Iran Admiral Shahram Irani, ya bayyana cewa, A halin yanzu Iran tana kara karfafa makamanta kuma da  izinin Allah ba da jimawa ba abokan gaba za su ga wani makami wanda zai ba su tsoro.”

Adimiral Shahram Irani ya kuma ce; Iran kasa ce mai hanyoyin ruwa masu muhimmnaci guda uku,kuma duk suna cikin muhimman hanyoyin ruwa guda 9 da ake da su a duniya,fitacce daga cikinsu shi ne mashigar ruwan Hurmuz.

Haka nan kuma Admiral Irani ya ce makiyan Iran dade suna sa ido akan wannan yankin,kamar yadda a tsakanin 1980 zuwa 1988 na kallafaffen yaki na biyu su ka so shimfida ikonsu a mashigar ruwan Hurmuz.

Babban kwamandan sojonin ruwan na Iran ya kuma yi Ishara da yadda makiya su ka rika yin hasashe da kirdado wanda yake zama kuskure akan makaman Iran da karfinta.

Admiral Irani ya kuma ce: Abinda makiya su ka tsammata shi ne cewa ta hanyar dogaro da amfani da jiragen yaki da wuraren harba makamai masu linzami daga doron ruwa za isa ta iya cimma manufofinta a cikin kankanen lokaci. Har ma da ayyana kwanaki da makwanni. A wannan lokacin wannan abinda Amurkan ta yi, ya zama abin yi wa dariya da isgili a cikin jami’o’in soja na duniya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted