Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato.
Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da kananan yara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da wadannan hare-hare tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu da kuma daukacin jama’ar Jihar Filato.
ACF ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-baci a wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga tare da hada kai da al’ummomin yankin domin dakile barazanar tsaro.
Haka kuma, kungiyar ta nemi gwamnati ta kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma kama wadanda ke da hannu a ta’asar.
Kungiyar ta jaddada bukatar wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato tare da bukatar a hada kai da shugabannin gargajiya, dattawa, kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile lamarin.
ACF ta kuma bukaci al’umma su rika bai wa jami’an tsaro bayanai kan duk wani abu da ka iya kawo matsala.